Wani Professor ne ya dawo Daga Aiki Sai ya iske Dandazon Mutane A
Kusa Da Kofar Gidanshi, Sai Ya wuce ba tare da ya tsaya ya tambayi meke faruwa ba, Yana Shiga Gida Sai ya dauko Jarida ya zauna akan Kujera ya fara Karantawa.
Zuwa Chan Sai Matarshi razo, tace "Kaga Taron wasu Mutane A Kofar Gida?"
Sai yace "Eh"
Sai tace "Wlh Gulmarka
Suke tayi, Sai yace "Wannan Kuma
SU YA-SHAFA"
Sai tace "Wai harma xewa sukeyi an yiwa wata Yarinya Ciki a Jami'ar da Kake Koyarwa"
Sai Yace "Wannan kuma Ita JAMI'AR YA SHAFA"
Sai Tace Kuma "Wai Sunce Kaine ma kayi
Mata Cikin"
Sai Yace "Wannan Kuma
NI-YA SHAFA"
Sai Tace "Kutumelesi! Toh Wlh Gidanmu zan Tafi"
Sai Yace "Wannan Kuma KE-YA SHAFA"😃
Duk Wanda Ya Karanta shima SHI YA SHafa..
No comments:
Post a Comment