Sahara ba abunda kakeji se gudun dawaki da
mutane wadanda zasu kai kimamin mutum 100
dikansu dakarun wani azzalumin sardine, dik
wannan angayar mutun biyu ake bi,
Gudu suke kamar zasu tashi sama can Naga
wata babbar mace Mai kimanin 40 yrs tafadi tana
haki, acan gefe wata yarinya tayi magana da
Sanyayyar murya ummy kitashi muje bamuda
lokacin Hutu yanzu, ahankali wadda aka kira da
ummy tace no Ajlal banida wani karfi ko zarafin
da Zan iya tashi, hawaye suka cika idon Ajlal
dasauri ta cakumi ummy tagoya sukayi cikin daji
sanadiyyar jin kukan dawakin na karasowa,
Haka suka cigaba Da yankar DAJI Ajlal na Goya
ummy tin tana bacci harta kasa.
tafiya sukayi Mai Nissan gaske baci basha.
Sunaji sunaganin manyan dabbobi se ummy ce
ke firgita amma dazaran suka nufuso zanga Ajlal
takalli sama tayi addua sann tadubi dabbar komin
girmanta dazaran suka hada ido da Ajlal Zata
koma yatsanta biyu take nuna su dashi yanxun
zasu juya ikon God kenan,
Kusan 3:00AM tayi musu basu Dena cin dajiba
dayaki karewa ko alamun mutum babu haka suka
samu gu suka kwanta bayan Ajlal ta musu
shimpida da haki tama ummy filo da cinyanta
sann ta tofesu da addua,
Kukan tsuntsaye ne yatadasu hakan yabasu
tabbacin safiya ta Waye ahankali Ajlal tajanye
jikinta taje yawon neman ruwa Amma bata
samuba dole tadawo tasame ummy har tafara
sallah ' gefe takoma tana kallon yanda ummynta
Ke kuka Acikin Sallah, bayan tagama ne tace
ummy kintashi lfy, kanta kawai tadaga mata
kasancewar tana lazimi ' taimama tayi tayi lullubi
da mayafinta ta tada sallah.
Suna gamawa suka dauki hanya ba Wanda kema
wani magana kowannensu da Abunda yake
sakawa aransa,
WANI Kuka kakeji da gurnani dasauri ummy ta
koma bayan Ajlal, wata babbar dabba ce dani
kaina bantaba ganin irintaba ko a film.
Ajlal takurawa wann dabbar Ido Sega ta taduka
murmushi Ajlal tayi Abbu kana Raye har yanzu
abbu kana Ina ne??
Hannun ummy taja suka nufi dabbar bamusu
suka hau gaban ummy nacigaba da faduwa ba
halin magana tinda abbu yabarmata wasiyar
cewa kartayi wa Ajlal Gardama idan taga wani
abun nafaruwa tsakanin ta da animals.
Haka suka hau dabbar segasu suntashi sama
tamkar tsuntsu Bai diresu ko inaba se wani dajin
Mai kyau da haske daga nan Yakoma inda yafito.
Aljal taja hannun ummy suka cigaba Da
tafiya......
Kwance yake kan carpet gefensa fadawa ne
Sekuma yan mata masu yimasa hidima.
Ahankali yake kutsura Apple rayuwarshi Fal take
bashida damuwar komai anahaka. sega calling
din Albina yashiga murmushi yayi Sannan yadaga
wayar gud morning beautiful one,
Murmushi tayi tareda gyara kwanciyar ta. Takara
hugging din pillow how are you my hero
Yabata amsa da fine ya exam. Alhamdulilah tace
tareda tambayar mutan gida haka suka cigaba
Da soyewa nikam Ina gefe Ina daukar tips na
love.
Tafiya sukayi Mai Nisan gaske dik acikin wannan
dajin ahankali suka fara jiyo kukan tsuntsaye
tareda sanyi hade da wani yanayi mai dadi. Ajlal
tadubi ummy tace mamana munkawo inda
mutane najiyo kamshin mutum. Ummy dai batace
uffan ba illah tayi murmushi
Da azama Ajlal Taja hannun ummy suka kutsa
cikin gurin ganin ruwa agurin da flowers Mai
kyau yasaka Ajlal yin wani irin Kara tareda sauri
taje gurin ruwan tasha tasha harta kasa tashi
ummy ma tasha
Aykuwa a take suka zube agurin bamai nun fashi
acikinsu
Tafe yake kan dokinsa yana cin Apple fadawa ba
biye dashi .
Zuma naji yafada dasauri aka basa yasha aka
basa tissue yagoge bakinsa Sannan suka cigaba
Da tafiya.
Acan nesa suka hango Kaman mutane Kuma da
alama matane kallonsu kawai yayi hakan yabasu
tabbacin meyake nufi dasauri sukayi kansu
tareda dubawa.
Ranka yadade suna nunfashi. Dan tanin yace ku
yayyafa musu ruwa. Haka kuwa akayi dakyar
suke nunfashi Dan tanin yabada order aje dasu
cikin gari sasashen yallabai kan sudawo
Mu Hadu a kashin Na biyu Domin jin yanda labarin ya kasance...
No comments:
Post a Comment