Wato Wani bafillace ne ya
shiga motar haya amma ya mance sunan garin
da
zai sauka. Yayi shiru yana famar tunanin yadda
za‘a yi ya tuno sunan garin da zai sauka.
Can sai yaron mota yace,“Modibbo kawo kudin
motar ka!“ Sai dan fulani yace,“Yo ai ni na
manshe
sunan garin da zan sauka.“
To dama a cikin motar akwai wani passenger mai
hakora zako-zako! Don haka dan fulani na
kallonsa
sai yacewa yaron motan,“amma dai sunan garin
yana kama da hakoran wanshan mutumin.“
Sai yaron motar ya kalli mutumin sannan yace
“KACAKO?“
Sai dan fulani yace “Aradu sunan garin ke nan
KASHAKO.
gaskiya na dara sosoai kundin nishadi allah yasaka
ReplyDelete