Wednesday, 5 April 2017

Labarin part 1,2,3, Da 4.

*MU KYAKYATA***
Wani saurayine yaje
xance, sai
budurwarsa ta nemi
ya bata labari, sai
yace to. amma labarin part 1, 2, 3,
da 4, sai tace ya
bata, saurayin ya
fara kamar haka
part 1: Wani mijine
da matarsa, suna cikin tafiya a mota,
can sai sukaxo
mararrabar hanya,
sai yacewa matar
wace hanya xamu
bi ? matar tace a'a dai maigida mubi
hanyar da ta bi
dama, aikuwa sai ya
kwashe ta da mari
yace nina ke tuka
motar ko kuwa ke? hanyar hagu xa
mubi, sai budurwar
ta saka dariya tace
amma wannan miji
akwai mugu,
saurayi yace saura part 2: suka bi
hanya suna tafiya
suka iso gun masu
saida kifi, maigida
ya siya musu,
matar tace maigida mai xa'ai dashi, yace
dapawa xakiyi,
aikuwa matar ta
xabgeshi da mari,
tace kaike girkin ko
ni?? Soyawa xanyi, Budurwar ta
kyalkyale da dariya,
tace amma ta
burgeni kaga sunyi
duro, saurayi yace
saura part 4, sai budurwar tace a'a
part 3 dai, saurayi
ya kwasheta da
mari, yace ni nake
bada labarin ko
ke...!! Toh wai idan kaine/
kece budurwar,
mexaki yiwa wannan
saurayin??

No comments:

Post a Comment