Saturday, 8 April 2017

KARKA GASKATASHI

Wata rana shehu yaje kasuwa, sai ya hadu da
wani
mutum shi kuma ya siyo tangaram cike da buhu,
sai yacema shehu, ka daukar man kayannan
nawa
ka kaiman gida, ni kuma zan sanar dakai wasu
abubuwa guda ukku da zasu amfaneka har
karshen
rayuwarka, shehu yace ya yarda,suna cikin tafiya
har sunyi kashi daya cikin ukku na tafiyarsu, sai
shehu yace ka fada min yanzu, sai mutumin yace,
na daya duk wanda yace maka da qoshi gara
yunwa karka gaskatashi, shehu yace to na biyu
fa?
Saiyace duk wanda yace maka da tafiya kan abin
hawa gara tafiya a qasa karka gaskatashi, bayan
sun isa kofar gidan mutumin sai shehu yace ka
fada min gudan, saiyace duk wanda yace zan
biyaka ladan daukar kayan nan karka gaskatashi,
sai shehu ya daga buhun tangaram ya rabkashi
da
kasa, sai yace duk wanda yace akwai sauran
tangaram mai rai a cikin buhunnan karka
gaskatashi

No comments:

Post a Comment