Tsohuwa na jin haka, sai ta mika wa 'Yar Sarki kwarashi da kayan saka. 'Yar Sarki ta karba, tsohuwa ta gwada mata yadda za ta yi. Ta fara sakawa ke nan, sai kuwa kwarashi ya soke mata hannu, nan take ta fadi kasa, sai barci. Ita kuwa mayya ta dauka mutuwa ta yi, ta fita abinta tana farin ciki, burinta ya cika.
Barci na dauke 'Yar Sarki, sai komai da ya ke cikin gidan barci ya dauke shi. Dawaki a barga suka soma barci, karnuka da tattabaru da suke kan rufin fada duka barci
ya dauke su. Wutar da take a dakin dafa abinci, ita ma ta daskare. Ga mai dafa abinci ta biyo kaza za ta kama ta yanka, ita
da kazar duk barci ya yi awon gaba da su. Wani dogari ma ya daga bulala ke nan zai labtawa wani bawa, duka barci ya kwashe su. Har wani dogari can gefe ya daga kofin zai sha ruwa, shi ma
barci ya dauke shi. Hatta kudaje da kwarin da suke cikin gidan nan duka barci ya dauke su. Sarki da Sarauniya na dawowa daga inda suka tafi, suna kutsa kai cikin fadar sai barci ya dauke su a kan
dawakinsu, duk da dawakin da 'yan rakiyarsu.
Labari ya watsu cikin gari, sai ya kasance babu mai matsawa kusa da fadar nan. Shekara bayan shekara, ciyayi da kayoyi da sarkakiya suka fito suka zagaye gidan. Duk shekara suna kara girma, har ya zamanto ba a iya ganin fadar, duk kayoyi da ciyayi sun rufeta. Labarin 'Yar Sarki mai
barci ya watsu ko'ina cikin duniya.
'Ya 'yan Sarakunan duniya da sadaukai da dama suka ta yiwo tattaki suna zuwa garin domin su ga 'Yar Sarki mai barci da kuma irin kyawonta da suke jin labari.
Amma duk wanda ya zo shiga gidan sai ya ga babu dama, domin kaya da sarkakiya sun rufe gidan, dole ya koma baya. Wasu kuma sukan yi karfin hali su kutsa kai
ciki, amma sai sarkakiya ta cukuikuye su, su kasa yin gaba su kasa yin baya, har yunwa ta kashe su.
Ana haka, wata rana wani
kyakkyawan Dan Sarki ya shigo garin, ya sauka gidan wani dan tsoho. Ya ce yana so dan tsoho ya kai shi fada su gaisa da Sarki. Dan tsoho ya ce babu Sarki a wannan
gari, shi da fadarsa duka an sihirce su suna can suna barci, har da wata 'yarsa wadda babu kamarta duk duniya a wurin kyau, an ce kuma ba za su farka ba sai bayan shekaru masu yawa, ni ma na ji wannan labari ne daga kakana.
Ko da Dan Sarki ya ji haka, sai ya ce wa dattijo ya nuna masa inda fadar take, yana so ya ga wannan abin al'ajabi. Tsoho ya yi masa kwatance da fadar, kuma ya gargade shi a kan kada ya kuskura ya ce zai shiga ciki, domin mutane da yawa sun halaka.
Dan Sarki na isa wurin da fadar take, maimakon ya ga ciyayi da sarkakiya da kayoyi, kamar yadda tsoho ya fada masa, sai ya tarar da fadar zagaye da furanni da ciyayi masu laushi. Ashe ranar ce 'Yar Sarki take cika shekara dari daidai tana barci. Dan Sarki ya kutsa kai cikin fadar, ya ga dukan mutane da dabbobin fadar barci suke yi.
Ya yi ta bi lungu-lungu, daki-daki, yana neman inda 'Yar Sarki take, har Allah ya sa ya kai ga dakin. Ya ganta kwance a kasa tana ta barci. Nan take ya kidime saboda
da tsananin kyanta da ya gani, sai ya ga duk kyanta da dan tsoho ya yi ta ruruta masa, bai fadi kashi ashirin cikin dari ba na kyanta.
Dan Sarki ya durkusa ya kura wa yarinya ido, sannan ya sunkuya ya sumbace ta(kiss) a kumatu. Yana sumbatar ta sai ta bude idonta, ta yi murmushi, nan take ta farka daga barcin shekara dari.
'Yar Sarki na farkawa, sai dukan abin da ke cikin gidan ya farka daga barci. Dawaki suka ci gaba da kukansu, tattabaru suka ci gaba da fiffikarsu, mai dafa abinci ta ci gaba da bin kaza za ta kama, bawa ya gudu don kada a dake shi da bulala, dogari ya ci gaba da shan ruwansa. Sarki da Sarauniya da 'yan rakiyarsu suka sauka daga kan dawakinsu. Rayuwa dai ta dawo a fadar kamar yadda take a farko. Aka yi ta mamakin wannan al'amari da ya faru.
Mutanen gari suka ci gaba da yi wa Sarkinsu biyayya, da ma can ba su nada wani sabon Sarki ba, saboda labarin adalci da taimakonsa da suka samu daga kakanninsu. Sarki ya aurar da 'Yarsa ga Dan Sarki, kuma ya yi murabus ya nada shi a matsayin sabon Sarki. Suka yi zamansu cikin jin dadi da kwanciyar hankali, har mai yanke jin dadi ta zo.
===| KARSHE LABARIN KENAN |===
Cikin labarin akwai ilmantarwa da fadakarwa,idan har kana biye dani a farkon labarin matar sarki Allah bai bata haihuwa ba,hakanan tai hakuri,karshe ta taimaki kifi wanda ta sanadiyar taimakon Allah ya azurtasu da haihuwa.
No comments:
Post a Comment