Saturday, 8 April 2017

Labarin Sarki Da Sarauniya A Garin Mayu

Wani Sarki ne da Sarauniyarsa suke mulki a wani gari mai yawan,mayu.Duk da cewa Sarkin nan da Sarauniyarsa babu abin da suka rasa na dukiya da jin dadin zaman duniya, amma Allah bai nufe su da
haihuwa ba tsawon shekaru, har tsufa ya fara sallamo ma su.
Ana nan wata rana, sarauniyar,nan ta fita bayan gari shan iska, ita kadai, har ta iso bakin wani rafi, sai kuwa ta ga wani dan
karamin kifi ruwa ya turo shi bakin gaba, ya yi, ya yi, ya koma ciki ya kasa har yana shirin mutuwa. Sarauniya ta ji tausayinsa ta dauke shi ta mayar
da shi cikin ruwa.
Bayan kifi ya yi nitso cikin ruwa, ranshi ya dawo, sai ya dago kansa saman ruwa ya ce da Sarauniya,
"Na san abin da ke damun ku, ke da mijinki, sakamakon taimakona
da kika yi, za ki haifi 'ya mace wadda babu kamarta a kyau duk
fadin duniyar nan, sai dai wani abin al'ajabi zai faru gare ta."
Yana gama fadin haka sai ya shige cikin ruwa abinsa.
Shekara ba ta kewayo ba sai da Sarki da Sarauniya suka haifi 'ya mace, wadda ba a taba ganin
kyakkyawa kamarta ba.
Da ranar suna ta kewayo, Sarki ya gayyato
manyan Sarakuna na duniya domin taya shi murna.
Ita kuma Sarauniya ta gayyato manyan mayun kasar su goma sha biyu.
Duk baki kowa ya hallara,
Sarakuna suka cika fada, mayu kuwa kowace ta zo tana sanye da jar hula da jajayen takalmi rike da
fararen sandunansu na tsafi.
Bayan an ci biki har an kusa watsewa, bakin Sarki suka bayar da kyaututtukan da suka kawo wa abokinsu.
Su kuwa mayu sai suka fara ba wa jaririya kyaututtukan sihiri. Ta
farko ta nuna ta da sandarta ta ce,
"Za ki zama kyakkyawa." Ta biyu
ta ce, "Za ki zama mai arziki." Ta
uku ta ce, "Za ki zama mai ilimi."
Ta hudu ta ce, "Za ki zama mai
tausayi da taimako."
Haka dai suka ci gaba da ba ta kyautuka har zuwa mayya ta goma sha daya. Har mayya ta sha
biyu za ta mike ta bayar da tata kyautar, sai aka ji wuri ya hargitse da kururuwa da hayaniya da iska.
Lokacin da wuri ya natsa, kamar daga sama sai aka ga wata mayyar ta bayyana a cikin taron,
tana sanye da bakar hula da bakaken takalmi da bakar sanda.Ashe an manta ba a gayyato ta ba wurin biki, ita kuwa ta ji haushin
wannan banbanci da aka nuna mata. Sai ta nuna jaririya da bakar sandarta ta ce, "Idan ki kai shekara goma sha biyar za ki soke
hannunki da kwarashin saka, nan take za ki mutu!" Tana fadar haka
sai ta yi wata irin dariyar keta, ta zama iska ta bace.
Hankali Sarki da Sarauniya ya tashi a kan wannan fata na mayya. Ga shi abin da suke nema shekara da shekaru sun samu amma burinsu
na barin zuri'a a duniya ba zai cika ba, 'yarsu za ta mutu tun kafin ta yi aure!
Nan da nan sai mayya ta goma sha biyu, wadda ba ta bayar da kyautarta ba, ta taso ta ce da Sarki
da Sarauniya, "Hakika wannan mayya da ta fita yanzu babbar matsafiya ce, babu mai iya tare
sihirinta a nan cikinmu. Amma ni, zan yi iyakar kokarina in rage masa karfi." Sai ta nuna jaririya da sandarta ta ce, "Idan ki ka cika shekara goma sha biyar, tabbas za ki soke hannunki da kwarashi,
amma ba za ki mutu ba, za ki kwanta barci wanda ba za ki farka ba sai bayan shekara dari."
Bayan an gama biki an watse, Sarki ya sa aka sanar da dukan mutanen gari duk wanda ya san
yana da kwarashi, kai koda allura ce, a fito da su. Aka tara kwarashi
da alluran garin gaba daya aka kona su. Sarki ya sa doka mai tsanani akan shigo da kwarashi ko allura a cikin garinsa.
Da 'yar Sarki ta fara tasawa, dukan kyautukan da mayun nan suka ba
ta, suka fara bayyana tare da ita.
Ga ta dai ta zama kyakkyawar da babu kamarta, ga hikima da
basira, ga tausayi, dukan abin da aka koya mata sau daya, shi ke nan ta rike shi.
A kwana a tashi har ta kai shekara goma sha biyar cif, a daidai lokacin ne kuma tafiya ta kama
Sarki da Sarauniya zuwa wani gari. Aka bar 'Yar Sarki a gida, ita da masu kulawa da ita. Da ta gaji
da zama sai ta tashi tana bi lungu-lungu na gidan domin ta mike kafafunta.
Ta zo wani lungu, sai ta
ga wani daki da marikin kofarsa ta zinariya. Ta kama marikin kofar
ta tura, sai kofar ta bude. Ta kutsa kai cikin dakin, sai ta ga wata 'yar tsohuwa, tukuf da ita, zaune a kan kujera tana saka.
Ta kura wa 'yar tsohuwa ido, ta ga yadda take ta surkulle da kwarashi, sai abin ya burgeta. Ta matsa kusa da 'yar tsohuwa ta gaisheta cikin ladabi, ta ce da ita tana so ta koyi yadda ake wannan
abu. Ashe ba ta sani ba, 'yar tsohuwar nan ita ce mayyar da ta yi mata fatar mutuwa bayan shekara goma sha biyar.
***

No comments:

Post a Comment