Sunday, 30 April 2017

*MU KYAKYATA***

Wani saurayine yaje
xance, sai
budurwarsa ta nemi
ya bata labari, sai
yace to. amma labarin part 1, 2, 3,
da 4, sai tace ya
bata, saurayin ya
fara kamar haka
part 1: Wani mijine
da matarsa, suna cikin tafiya a mota,
can sai sukaxo
mararrabar hanya,
sai yacewa matar
wace hanya xamu
bi ? matar tace a'a dai maigida mubi
hanyar da ta bi
dama, aikuwa sai ya
kwashe ta da mari
yace nina ke tuka
motar ko kuwa ke? hanyar hagu xa
mubi, sai budurwar
ta saka dariya tace
amma wannan miji
akwai mugu,
saurayi yace saura part 2: suka bi
hanya suna tafiya
suka iso gun masu
saida kifi, maigida
ya siya musu,
matar tace maigida mai xa'ai dashi, yace
dapawa xakiyi,
aikuwa matar ta
xabgeshi da mari,
tace kaike girkin ko
ni?? Soyawa xanyi, Budurwar ta
kyalkyale da dariya,
tace amma ta
burgeni kaga sunyi
duro, saurayi yace
saura part 4, sai budurwar tace a'a
part 3 dai, saurayi
ya kwasheta da
mari, yace ni nake
bada labarin ko
ke...!! Toh wai idan kaine/
kece budurwar,
mexaki yiwa wannan
saurayin??

πŸ˜‚πŸ˜‚MUSHA DARIYAπŸ˜‚πŸ˜‚

Wani Professor ne ya dawo Daga Aiki Sai ya iske Dandazon Mutane A
Kusa Da Kofar Gidanshi, Sai Ya wuce ba tare da ya tsaya ya tambayi meke faruwa ba, Yana Shiga Gida Sai ya dauko Jarida ya zauna akan Kujera ya fara Karantawa.
Zuwa Chan Sai Matarshi razo, tace "Kaga Taron wasu Mutane A Kofar Gida?"
Sai yace "Eh"
Sai tace "Wlh Gulmarka
Suke tayi, Sai yace "Wannan Kuma
SU YA-SHAFA"
Sai tace "Wai harma xewa sukeyi an yiwa wata Yarinya Ciki a Jami'ar da Kake Koyarwa"
Sai Yace "Wannan kuma Ita JAMI'AR YA SHAFA"
Sai Tace Kuma "Wai Sunce Kaine ma kayi
Mata Cikin"
Sai Yace "Wannan Kuma
NI-YA SHAFA"
Sai Tace "Kutumelesi! Toh Wlh Gidanmu zan Tafi"
Sai Yace "Wannan Kuma KE-YA SHAFA"πŸ˜ƒ

Duk Wanda Ya Karanta shima SHI YA SHafa..

Saturday, 22 April 2017

ANGO MAI FITSARIN KWANCE


wani ne yayi aure yana fitsarin kwance, ya kwanta bacci sai yayi fitsari ya rasa yadda zaiyi kawai sai ya tada matar yace mata " idan kece kikayi mafarkin kuraπŸ˜ˆπŸ‘Ώ da zaki😸😺da damisa😾😾su biyoki ya zakiy?sai matar tace"😳😳tabdijam ai sai nayi zawo, sai angon yace ashe ni jarumine fitsari kawai nayiπŸ˜…πŸ˜€πŸ˜€

MUSHA DARIYA!!! Wata yarinya ce taga hoton babanta lokacin ana samartaka an ci tabarau, ga uban gashi da matsattsiyar riga, wandon nan fantalo; kawai sai mamanta taji ta tana dariya. Sai uwar ta tambayeta "menene ya ke saki dariya haka?" Yarinya kuwa ta ce "Hoton baba na gani lokacin yana dan iska"!!!


Wata yarinya ce taga hoton babanta lokacin ana samartaka an ci tabarau, ga uban gashi da matsattsiyar riga, wandon nan fantalo; kawai sai mamanta taji ta tana dariya. Sai uwar ta tambayeta "menene ya ke saki dariya haka?"
Yarinya kuwa ta ce "Hoton baba na gani lokacin yana dan iska"!!!

Asha dariya


🚢Wani yarone πŸ™Žbabarsa ta aikeshi, shago da naira ashirin goma goma guda biyuπŸ’Ά,suga na goma ganyenshayi na goma,da yaran yaje shagon sai yasamu waje yazauna yana kuka, sai aka tambayeshi lafiya yake kuka ko kudinne suka fadi, sai yaron yace a'a mantawa yayi wacce gomace ta suga waccece ta ganyenshayi 

KARYA FURE TAKE.

πŸ™ˆπŸ™ˆπŸ™ˆπŸ™ˆπŸ™ˆπŸ™ˆ wani abokin ango ne aka gayyace shi daurin auren abokin sa bai jeba washegari sai suka hadu da angon suka gaisa sai yace kai amma daurin auren yayi mutane ina ta miko maka hannu baka ganiba sai yace ai an daga sai wani satin 

ANGO DA AMARYA:......

 Wani Ango ne yakai karar Amaryaa police station sai aka turasu gaban DPO dazuwan su sai DPO yazubawa amarya ido kuru kuru DPO yace waye mai laifin ne sai aka nuna amarya yakalle ta takalleshi yace kai wannan batada laifi kokadan ace DPO yaga mai kyekkewagata fara tasha lalle sai DPO yace bazai saurari karar yauba sai gobe asata a sel da dare yayi sai DPO ya dauketa yaje ya kwana da ita da asubah yamedata sel da safe sai ga mijinta yazo sai DPO yace kaikuma mace kamar wannan laifinme tayi har kawota wurin police sai yace yawo takeyi harta debo HIV tasakamin.

Thursday, 20 April 2017

MUSHA DARIYA

πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚
Wani saurayi ne a makaranta, ya shiga dakin karatu (library) da shigarsa sai ya hango wata kyakkyawar budurwa a gefe zaune ita kadai, kun san halin samari da son hulda da 'yan mata masu kyau, gogan naku sai ya isa inda take yai mata sallama, sai yace mata na ganki ke kadai zaune, shine naga bai dace kyakkyawar mace kamarki ta zauna cikin kadaici ba, shine nace bari na zo na tayaki hira, kawai sai budurwar ta daga murya da karfi  tace "KA GA MALAM NI BA 'YAR ISKA BA CE DA ZAKA CE IN BIKA DAKINKA IN KWANA KAJE CAN KA NEMI 'YAR ISKA IRINKA" gaba daya hankalin mutanen dake wurin ya dawo kansu, saurayin yaji kamar kasa ta tsage ya shige ciki don kunya,
bayan mintuna kadan sai budurwar tazo inda yake tayi kasa da murya tace masa ina karatun psychology ne na iya karantar abinda ke ran mutum, ko ban tambayeka ba na san kaji kunya da abinda nayi ma, saurayin shima sai ya buda bakinsa da karfi yace "KWANA DAYA A DUBU HAMSIN (50000) GASKIYA SUNYI YAWA, HALA AN FADA MAKI SATA NAKE YI?" gaba daya hankalin mutanen wurin ya sake dawowa kansu, wasu suka dinga yi mata dariya suna cewa ashe duk kanwar ja ce, saurayin ya kalleta shima yayi kasa da murya yace mata karki damu ina karatun law ne na sanin  hanyoyin kama mutum idan yayi min laifi.πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚

Don Allah A Cikinsu Wa Yafi qwarar Wani?

LABARIN WASU MATAFIYA DA ALJANI A SAHARA!!!!

Wasu mutane ne su uku, suna tafiya � �
�a sahara kowane daga cikin su ya galabaita
da yunwa da kishirwa sun wahala matuka.
Gashi ko alamar gari basu ganibaπŸ‘ πŸ‘
basusan lokacin fitarsu daga wannan saharar ba
don haka harsun faratunanin mutuwa kwatsam
sai ga wata kwalba agaban su sunyi tunanin
ruwa ne acikinta Amma ina. suna bude
kwalbar wani hayaki ya tashi sama, hayakin
nagama fita sai ya hade waje daya, sai ga wani
Aljani kato agaban su. �Nan take
aljanin yayi wata mahaukaciyar dariya yace
kowanne acikinku yafadi bukatarsa kowacce irice
zan biya masa sakamakon budeni da kukayi
daga wannan kwalba. Aikuwa sai farin ciki ya
rufesu gaba daya sai aka tambayi na
farko �mai kake so...? Sai yace inaso
akaini "DUBAI" abudemin kasuwanci sannan
acikamin katuwar kwantena da kudi kusa da
shagwan kasuwanci na. Sai aljani yace ba
wata....? Yace eh. Sai Aljani yace to
shikenan rufidonka yanbudewaπŸ‘ ya ganshi
Adubai dukkan abubuwan da ya bukata.
Said akazokan nabiyu �Me kake so...? Sai
yace � a kaini America ayimin katon gida da
motoci da kudi masu yawanda bazan iya
karardasbaAljani yace bawani...? yace eh.
Aljani yace rufe idonka yanbudewaπŸ‘ ya
ganshi a America da duk abinda yabukata.
Sai akazo kan na karshe Me kake so...Yace
Akawo masa ruwa, aka kawo yasha ya wanke
jikinsa, saaljani yace sai mai kakeso...? Sai
yace bukata tkarshe Adawomin da 'yan uwana
mucigaba da tafiya. � � �Aljani yace
itace bukatarka ta karshe..? Yace eh.
Yanarufe bakinsa sai gasu kowanne an dawo
dashi cikisahara Aljani yabace yatafi
abinsa.
Idan Da Kai
acikin matafiyan nan mezaka yiwa abokin
tafiyarku na uku �............?

KAIMA ABAKA

wani bawan Allah ne ya auri bebiya, kullum idan dare yayi saiyazo gurin amaryarsa πŸ‘‰πŸ‘©‍πŸ’Ό
Itakuma saita dunga gudunshi harta fada masa cewa *ita ba 'yer iskaba ce* da mijin yagaji da halinta saiya koreta yace tatafi gidansu,

Dataje gida sai iyayenta suke tambayar ta abinda yahadasu da mijinta,

*saitabasu labarin abinda yafaru tundaga farko har qarshe*

Sai mamanta tayi mata fada tace kada taqara hanashi duksanda yake buqata tabashi,

Bayan anyi musu sulhu takoma gidan ta πŸ€“πŸ€“πŸ€“

Ango yazo (1) washe gari ma yasake

*Amarya taji dadi sosai*  

Wata rana Abokin Ango yakawo ziyara sai bebiyar Amarya tazo gurin Abokin angon  tace mai
 *kaima abaka*



Idan Kaine Angon mezakayi mata ?????


MUSHA DARIYA

wani malamine ya tambayi yan class menene love ? sai wata yariya tace love is a chemical substance that react between two heart sai yace are you stupid sai tace stopid is a person who ask the meaning of love...

Kaza Da Akuya

Watarana angama ruwan sama kaza da kawarta akuya suna tafiya agefen titi sai wani mai mota🚘 yawuce aguje harya fallatsa musu ruwan kwata sai kazaπŸ“ tace Ji yadda suke gudu kamar wasu awaki🐐🐐 sai akuya🐐 tadanyi murmushi tace shiyasa suke mutuwa kamar kajiπŸ“πŸ“πŸ“
πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚

Saturday, 15 April 2017

☆☆☆LABARIN SADAUKI☆☆☆

KASHI NA UKU......
Jekadiya Zaune agaban mama tace ranki yadade
mutanenan da aka tsinto suna bukatar taimako
Mama tagyara zama kamar name kenan, jekadiya
tace ga dukkan alamu wahala ce tafidda su daga
inda suke, sa'Annan sunce ataimaka abasu
kowani irin ayki zasu iya sudai burinsu su samu
masauki da abunci basu damu da albashiba.
Mama tace Allah sarki zanga Ajlah idan yana
bukatar hadimai abasa nagan ya kori hadimarshi
mace. Jekadiya tace hakane Allah ya biya
Ameen
Kwance yake yana karatun jarida karar kibiya tayi
yawa hakan yafidda shi waje tsaye yayi yana
kallon Nura dake faman fafatawa da yaran Ajlah.
Har zai koma ciki, Nura yace hey maza SADAUKI
jarumin maza kozaka Dan Dana ne,
Murmushi yayi yagirgiza kanshi Sannan yace
Nura ka rike girmanka har kullum Ina gaya maka
cewa naga yayi gaba na baya sea labari.
Nura yace adane wlh yanzu kam bana Jin akwai
wani jarumin dazai iya gwabzawa dani, murmushi
yayi yanufi hanyar ciki, kamar mafarki yagan
ansako masa tasoki hannun rigarshi Sannan
Kuma ta kafe da gina zai juyo aka sake halbo
wani, cike da bacin rai yazare su tareda jifa da
cup dinda Ke hannunsa yanufi Nura,
Nura na ganin haka yayi murmushin mugunta
yanufesa bil-haqqi fafatawa takasance tsananin
jaruman biyu, bawanda yayi nasarar kauda wani
acikinsu, can Nura dayaga bada karfi yakeba
aykuwa ya manna masa takobi a gefen hannu
Tini jini yafara sintiri, fadawansa suka yo caaa a
take yadaga musu hannu alamar su dakata
tareda soka takobi akasa, sann ya yaga rigarshi
dik kaurinta yadaure inda jinin Ke zuba,
Dubi daya na masa nakoma aguje yanda yasauya
alokaci guda ya rikida yazama wani irin lion,
takobinsa yajanyo yacigaba da fafatawa da Nura
tuni yacire hular dake kan nura ciki Harda uwar
sumar dayake tarawa, sann ya wangale Abun
dasuke karawa ahannu ahaka yacigaba da ketar
nura seda yazare dik wani Abu dake jikinsa na
karfe baibarsaba suka cigaba wani tsalle yayi
yadoki nura awuya segashi a kasa hakan yabasa
damar cira takobinsa da nufin soka masa.
Karka aykata hakan aka fada dawata muryar ta
dattawa, tsohone dazai kai kimanin 70 yrs cikin
shiga ta alfarma se wasu mazan dasuke kamar
twins suna gefensa kowannensu yana Mai jin
haushin SADAUKI dakuma rashin kasance dansa
ne yakeda wannan karfin da jarumta,
Hakan yasa dole yajefar da takobinsa sann ya
cakumi wuyan Nura, "ko a bacci kayi mafarkin
zaka fafata dani to kace karya ne, Ni Ajlah ibn
Muhammad ibn Umar bawanda ya isa yaja dani
Ni jarumi ne nikuma SADAUKI ne SADAUKIn
ragwayen maza yana kai nan yajuya afusace ya
nufi room dinshi dasauri Dan tanin yarufa masa
baya
Dan tanin ya bude fridge yadauko masa gorar
ruwan faro yamika masa ya karba ya ajiye Dan
tanin plss leave me for while I want be alone Dan
tanin yace ok sir wish you happy now and for
ever.
Thanks yafada tareda fadawa kan gadonsa seda
yaji relief sann ya tashi yadora ruwan zafi
dakanshi yayi dressing gurinda yaji ciyo sann
yaje toilet a gurguje yayi wanka tareda alwala
yafito waje Dan bin jam'I
Anan suka Hade kabir dasauri ya sakar masa
murmushi hey kabir saukar yaushe, kabir yace
wlh jiya cikin dare.
Ajlah yace toya hanya ya skull hup dae komai
fyn. Kabir yace insha Allah kagama da takardata
nazo har Sun daukeni ayki a can but bana
tunanin Mai martaba zai bari,
Ajlah yayi murmushi hakane fah gamu Nan daga
gida se company's bara abar mutun da abunda
ya karanta ba,
Kabir yace banga kana shirye2 dawowan Albina
ba " cikin rashin fahimta yace Kaman yah"? Kabir
yace kaddai kacemun baka San da zuwanta ba "
Ajlah yace agunka naji myb zatai surprising Dina
ne ' yes hakane inji kabir, Haka suka cigaba da
fira har kofar masallaci
Waye Ajlah miye asalinsu da sarautarsu kubi yoni
danji......

Thursday, 13 April 2017

Tambaya... Maza Kawai Banda Mata

IN KAINE WANNE XAKA XABA❓❓
Wani mutum  ne yayi lepi sai dan sanda🏻ya kama shi ya kaishi kotuπŸ› sai Alkalin nan yace xe yanke masa hukunci acikin biyu ya xabi daya: ko dai a kaishi prison yayi shekara 10 ko kuma a tsareshi har se Arsenal ta dau Champion a sake shi....... In kaine wanne xaka xaba❓❓ KU TUTTURA GROUPS DOMIN MUJI RA'AYOYIN MUTANEπŸ˜‚πŸ˜‚

Tuesday, 11 April 2017

☆☆☆LABARIN SADAUKI☆☆☆

KASHI NA BIYU
Katon gida Wanda yawanashi kadai abun kallo ne
yakai girman wani karamun Kauye.
Filine babba Wanda zaisaka tsawon tafiya acan
nesa nake hango motoci tareda hadiman gidan
daga maza zuwa mata, tafiya Mai Dan nisa
takaisu ga gate din gidan idan kashiga flowers ne
birjir gwanin sha'awa se wasu kofofi kusan uku
kowacce kofa katuwar gaskece sa'Annan ginine
na sarauta ta tsakiyar tafi kowaci girma da kyau
kowace kofa akwai fadawa Akanta tareda
soldiers,
Kofar tsakiya nagan sunbi tareda shugabansu
direct part dinshi aka wuce dashi batareda yabi
takansuba.
Gurin matar Mai martaba sukaje wato Nana
hauwa wadda kowa me kira da mama, Dan tanin
yayi sallama jekadiyarta ce ta amsa se masu
yimata hidima. Kozan samu ganin mama kuwa
tambayar da jefo kenan.
Jekadiya tace ko alama mama nada baki sedai
ko Gobe, Dan tanin yace just two minute fah,
afusace jekadiya tace wannan Kuma kaikasan
mekake cewa.
Murmushi yayi Allah huci ranki gwaggoji, harya
juya Sega mama tafito.
Kasa ya zube yana kwasar gaisuwa, mama tace
Dan tanin bajabakaji koh, saunawa Zan gayama
bana San Ana dukamun nida kai dik matsayinmu
daya agurin Allah it myb ma kafini daraja if kafini
tsoron Allah. Jekadiya tace habawa yoshe Kuma
Dan tanin zaifiki tsoron Allah, mama tace kinjiki
dawani zance Ke harkullum kina tsoron gayamun
gaskiya bana son irin hakan akiyaye gaba, cike
da mutuwar jiki jekadiya tace ALLAH ya huci
ranki shugabata dasauri mama tajuyo mekikace
jikin jekadiya yadau bari tace amun afuwa ranki
yadade cike da takaici ta girgiza kai tamaida
dubanta ga Dan tanin dayake murmushi
Meke tafe dakai? Dan tanin yabata lbrn abunda
suka tsinta wato Ajlal da ummynta. Mama tace
subhanallah shine tindazu Kayi shiru baka saurin
gaya mun ba Ina suke din ' Dan tanin gaba mama
baya har inda suke wani zaure fadawa na musu
ferfita
Mama tace maza akaisu side dinta jekadiya
kikula dasu abasu sutura da abunci idan kinga da
matsala contact me Inji mezanyi akai tana kai
nan tawuce wasu hadiman suka bita.....
Daki aka basu tareda kyakkyawan masauki bacci
suke hakan yasaka aka kyalesu se kusan magrib
suka farka atare dasauri wata hadimar takawo
musu abunci kyada kai sukayi Ajlal tace Ina
mukene ko mundawo gidane.?
Hadimar tace wannan amsa se wadanda suka
tsinto ku yanzu dik ba wann ba kuci abunci
kucanza kaya sann muji lbrn ku, Ajlal zatayi
magana ummy tadafata "halas binti " it's ok
daughter.
Gyda kai tayi tace abasu ruwa zasu wanke
bakinsu tukun.
Bayan sun gama sukaci abunci bana wasaba
sann sukayi alwala saboda ramakon salloli dake
kansu. After sungama sukayi wanka aka basu
sutura suka saka wani baccin ne yakara kwashe
su........
impossible taya za'ace ba'agansuba bayan
antsince Dan kwalin Aljal.
WANI bafade Naga yasunkuyadda kai kasa yace
Allah huci zuciyanka wlh ba irin neman daba
muyi musuba Amma ba'a samesuba ko wani Abu
Mai kama da su bamu samuba Se wann Dan
kwalin. Sedai kuwa idan dabbobi suka cinye su.
How comes dabba bata taba Ajlal bare ta
cinyeta,
I know something happened I know dunkule
hannunshi yayi tareda dukan kujera too bad...
Get out of here. Dasauri mugu yafita kan ya
ballasa
Mom tashigo dakin relax bom boy komai zaiyi
dai2.
Mom..... shiiiii tafada tareda nuna masa gado
dole yazauna badan yasoba,
Haba shamsu meyasa zaka tada hankalinka akan
abunda yarigada yagama faruwa, matukar
banaso ba Tokuwa ba Wanda ya isa yaja damu
barema wani zancen Ajlal yo Ina Mai Goya mata
baya din?
Na wulgasa lafira Ina jarumatarshi dawani
kwarewarshi yo Ina baiwar dayake taqama daita,
ina baiwar yar tashi dik suntafi abanza Dan
basazu amfanesu dakomai ba,
Shamsudden ya nisa tareda yes hakane but
momy matukar wannan awarwayo yana hannun
Ajlal ratuwarmu tab take da barazana sa'Annan
koyaushe mulkinnan zai iya juyawa akanmu,
mutane gari sunyi obey da wasiyyar da Abbu
yabayar ' don't worry son zanyi clearing komai
it's my pleasure.. okay yadaga kai fuskarka
bayabo ba fallasa.....
Mu hadu  a kashi na uku.

Monday, 10 April 2017

☆☆☆LABARIN SADAUKI☆☆☆

Sahara ba abunda kakeji se gudun dawaki da
mutane wadanda zasu kai kimamin mutum 100
dikansu dakarun wani azzalumin sardine, dik
wannan angayar mutun biyu ake bi,
Gudu suke kamar zasu tashi sama can Naga
wata babbar mace Mai kimanin 40 yrs tafadi tana
haki, acan gefe wata yarinya tayi magana da
Sanyayyar murya ummy kitashi muje bamuda
lokacin Hutu yanzu, ahankali wadda aka kira da
ummy tace no Ajlal banida wani karfi ko zarafin
da Zan iya tashi, hawaye suka cika idon Ajlal
dasauri ta cakumi ummy tagoya sukayi cikin daji
sanadiyyar jin kukan dawakin na karasowa,
Haka suka cigaba Da yankar DAJI Ajlal na Goya
ummy tin tana bacci harta kasa.
tafiya sukayi Mai Nissan gaske baci basha.
Sunaji sunaganin manyan dabbobi se ummy ce
ke firgita amma dazaran suka nufuso zanga Ajlal
takalli sama tayi addua sann tadubi dabbar komin
girmanta dazaran suka hada ido da Ajlal Zata
koma yatsanta biyu take nuna su dashi yanxun
zasu juya ikon God kenan,
Kusan 3:00AM tayi musu basu Dena cin dajiba
dayaki karewa ko alamun mutum babu haka suka
samu gu suka kwanta bayan Ajlal ta musu
shimpida da haki tama ummy filo da cinyanta
sann ta tofesu da addua,
Kukan tsuntsaye ne yatadasu hakan yabasu
tabbacin safiya ta Waye ahankali Ajlal tajanye
jikinta taje yawon neman ruwa Amma bata
samuba dole tadawo tasame ummy har tafara
sallah ' gefe takoma tana kallon yanda ummynta
Ke kuka Acikin Sallah, bayan tagama ne tace
ummy kintashi lfy, kanta kawai tadaga mata
kasancewar tana lazimi ' taimama tayi tayi lullubi
da mayafinta ta tada sallah.
Suna gamawa suka dauki hanya ba Wanda kema
wani magana kowannensu da Abunda yake
sakawa aransa,
WANI Kuka kakeji da gurnani dasauri ummy ta
koma bayan Ajlal, wata babbar dabba ce dani
kaina bantaba ganin irintaba ko a film.
Ajlal takurawa wann dabbar Ido Sega ta taduka
murmushi Ajlal tayi Abbu kana Raye har yanzu
abbu kana Ina ne??
Hannun ummy taja suka nufi dabbar bamusu
suka hau gaban ummy nacigaba da faduwa ba
halin magana tinda abbu yabarmata wasiyar
cewa kartayi wa Ajlal Gardama idan taga wani
abun nafaruwa tsakanin ta da animals.
Haka suka hau dabbar segasu suntashi sama
tamkar tsuntsu Bai diresu ko inaba se wani dajin
Mai kyau da haske daga nan Yakoma inda yafito.
Aljal taja hannun ummy suka cigaba Da
tafiya......
Kwance yake kan carpet gefensa fadawa ne
Sekuma yan mata masu yimasa hidima.
Ahankali yake kutsura Apple rayuwarshi Fal take
bashida damuwar komai anahaka. sega calling
din Albina yashiga murmushi yayi Sannan yadaga
wayar gud morning beautiful one,
Murmushi tayi tareda gyara kwanciyar ta. Takara
hugging din pillow how are you my hero
Yabata amsa da fine ya exam. Alhamdulilah tace
tareda tambayar mutan gida haka suka cigaba
Da soyewa nikam Ina gefe Ina daukar tips na
love.
Tafiya sukayi Mai Nisan gaske dik acikin wannan
dajin ahankali suka fara jiyo kukan tsuntsaye
tareda sanyi hade da wani yanayi mai dadi. Ajlal
tadubi ummy tace mamana munkawo inda
mutane najiyo kamshin mutum. Ummy dai batace
uffan ba illah tayi murmushi
Da azama Ajlal Taja hannun ummy suka kutsa
cikin gurin ganin ruwa agurin da flowers Mai
kyau yasaka Ajlal yin wani irin Kara tareda sauri
taje gurin ruwan tasha tasha harta kasa tashi
ummy ma tasha
Aykuwa a take suka zube agurin bamai nun fashi
acikinsu
Tafe yake kan dokinsa yana cin Apple fadawa ba
biye dashi .
Zuma naji yafada dasauri aka basa yasha aka
basa tissue yagoge bakinsa Sannan suka cigaba
Da tafiya.
Acan nesa suka hango Kaman mutane Kuma da
alama matane kallonsu kawai yayi hakan yabasu
tabbacin meyake nufi dasauri sukayi kansu
tareda dubawa.
Ranka yadade suna nunfashi. Dan tanin yace ku
yayyafa musu ruwa. Haka kuwa akayi dakyar
suke nunfashi Dan tanin yabada order aje dasu
cikin gari sasashen yallabai kan sudawo
Mu Hadu a kashin Na biyu Domin jin yanda labarin ya kasance...

Fulani sai a Hankali fa

Wato Wani bafillace ne ya
shiga motar haya amma ya mance sunan garin
da
zai sauka. Yayi shiru yana famar tunanin yadda
za‘a yi ya tuno sunan garin da zai sauka.
Can sai yaron mota yace,“Modibbo kawo kudin
motar ka!“ Sai dan fulani yace,“Yo ai ni na
manshe
sunan garin da zan sauka.“
To dama a cikin motar akwai wani passenger mai
hakora zako-zako! Don haka dan fulani na
kallonsa
sai yacewa yaron motan,“amma dai sunan garin
yana kama da hakoran wanshan mutumin.“
Sai yaron motar ya kalli mutumin sannan yace
“KACAKO?“
Sai dan fulani yace “Aradu sunan garin ke nan
KASHAKO.

Ci Gaban Labarin Sarki Da Sarauniya A Garin Mayu

Tsohuwa na jin haka, sai ta mika wa 'Yar Sarki kwarashi da kayan saka. 'Yar Sarki ta karba, tsohuwa ta gwada mata yadda za ta yi. Ta fara sakawa ke nan, sai kuwa kwarashi ya soke mata hannu, nan take ta fadi kasa, sai barci. Ita kuwa mayya ta dauka mutuwa ta yi, ta fita abinta tana farin ciki, burinta ya cika.
Barci na dauke 'Yar Sarki, sai komai da ya ke cikin gidan barci ya dauke shi. Dawaki a barga suka soma barci, karnuka da tattabaru da suke kan rufin fada duka barci
ya dauke su. Wutar da take a dakin dafa abinci, ita ma ta daskare. Ga mai dafa abinci ta biyo kaza za ta kama ta yanka, ita
da kazar duk barci ya yi awon gaba da su. Wani dogari ma ya daga bulala ke nan zai labtawa wani bawa, duka barci ya kwashe su. Har wani dogari can gefe ya daga kofin zai sha ruwa, shi ma
barci ya dauke shi. Hatta kudaje da kwarin da suke cikin gidan nan duka barci ya dauke su. Sarki da Sarauniya na dawowa daga inda suka tafi, suna kutsa kai cikin fadar sai barci ya dauke su a kan
dawakinsu, duk da dawakin da 'yan rakiyarsu.
Labari ya watsu cikin gari, sai ya kasance babu mai matsawa kusa da fadar nan. Shekara bayan shekara, ciyayi da kayoyi da sarkakiya suka fito suka zagaye gidan. Duk shekara suna kara girma, har ya zamanto ba a iya ganin fadar, duk kayoyi da ciyayi sun rufeta. Labarin 'Yar Sarki mai
barci ya watsu ko'ina cikin duniya.
'Ya 'yan Sarakunan duniya da sadaukai da dama suka ta yiwo tattaki suna zuwa garin domin su ga 'Yar Sarki mai barci da kuma irin kyawonta da suke jin labari.
Amma duk wanda ya zo shiga gidan sai ya ga babu dama, domin kaya da sarkakiya sun rufe gidan, dole ya koma baya. Wasu kuma sukan yi karfin hali su kutsa kai
ciki, amma sai sarkakiya ta cukuikuye su, su kasa yin gaba su kasa yin baya, har yunwa ta kashe su.
Ana haka, wata rana wani
kyakkyawan Dan Sarki ya shigo garin, ya sauka gidan wani dan tsoho. Ya ce yana so dan tsoho ya kai shi fada su gaisa da Sarki. Dan tsoho ya ce babu Sarki a wannan
gari, shi da fadarsa duka an sihirce su suna can suna barci, har da wata 'yarsa wadda babu kamarta duk duniya a wurin kyau, an ce kuma ba za su farka ba sai bayan shekaru masu yawa, ni ma na ji wannan labari ne daga kakana.
Ko da Dan Sarki ya ji haka, sai ya ce wa dattijo ya nuna masa inda fadar take, yana so ya ga wannan abin al'ajabi. Tsoho ya yi masa kwatance da fadar, kuma ya gargade shi a kan kada ya kuskura ya ce zai shiga ciki, domin mutane da yawa sun halaka.
Dan Sarki na isa wurin da fadar take, maimakon ya ga ciyayi da sarkakiya da kayoyi, kamar yadda tsoho ya fada masa, sai ya tarar da fadar zagaye da furanni da ciyayi masu laushi. Ashe ranar ce 'Yar Sarki take cika shekara dari daidai tana barci. Dan Sarki ya kutsa kai cikin fadar, ya ga dukan mutane da dabbobin fadar barci suke yi.
Ya yi ta bi lungu-lungu, daki-daki, yana neman inda 'Yar Sarki take, har Allah ya sa ya kai ga dakin. Ya ganta kwance a kasa tana ta barci. Nan take ya kidime saboda
da tsananin kyanta da ya gani, sai ya ga duk kyanta da dan tsoho ya yi ta ruruta masa, bai fadi kashi ashirin cikin dari ba na kyanta.
Dan Sarki ya durkusa ya kura wa yarinya ido, sannan ya sunkuya ya sumbace ta(kiss) a kumatu. Yana sumbatar ta sai ta bude idonta, ta yi murmushi, nan take ta farka daga barcin shekara dari.
'Yar Sarki na farkawa, sai dukan abin da ke cikin gidan ya farka daga barci. Dawaki suka ci gaba da kukansu, tattabaru suka ci gaba da fiffikarsu, mai dafa abinci ta ci gaba da bin kaza za ta kama, bawa ya gudu don kada a dake shi da bulala, dogari ya ci gaba da shan ruwansa. Sarki da Sarauniya da 'yan rakiyarsu suka sauka daga kan dawakinsu. Rayuwa dai ta dawo a fadar kamar yadda take a farko. Aka yi ta mamakin wannan al'amari da ya faru.
Mutanen gari suka ci gaba da yi wa Sarkinsu biyayya, da ma can ba su nada wani sabon Sarki ba, saboda labarin adalci da taimakonsa da suka samu daga kakanninsu. Sarki ya aurar da 'Yarsa ga Dan Sarki, kuma ya yi murabus ya nada shi a matsayin sabon Sarki. Suka yi zamansu cikin jin dadi da kwanciyar hankali, har mai yanke jin dadi ta zo.
===| KARSHE LABARIN KENAN |===
Cikin labarin akwai ilmantarwa da fadakarwa,idan har kana biye dani a farkon labarin matar sarki Allah bai bata haihuwa ba,hakanan tai hakuri,karshe ta taimaki kifi wanda ta sanadiyar taimakon Allah ya azurtasu da haihuwa.

Ina da laifi????

Jiya a Facebook naga wata yarinya tayi postn tace," Duka maza Awakine .."
Sai na tambayeta," Shin yau kinba Mahaifin ki ciyawa ☘ , sannan zaki iya auren Tinkiya irin Mahaifin ki???"
Ka wai sai tayi blocked dina...
Yau da sanyi safiya na hau whatsapp sai naga wani saurayi yayi postn a wani grp yace," Duka mata kamar katin waya suke, idan ka saya ka loda, sai ka yada katin ya gama amfani"..
Sai na tambaye shi," Shin mahaifiyar ka wace network ce? MTN, GLO ko 80SLT??..
Wallahi shima sai yayi blocked dina...
To meye Laifin Malam anan??

LABARIN DAN SANDA

Wani dan sanda ne sunje patrol din dare sun dawo sai yace da yan uwan sa shi zai sauka anan sai ya karasa gida bayan ya sauka yana tafiya sai yaga wani mutum da katifa sai yace masa kai ina zakaje da KATIFA mutumin yayi ta masa magiya don ya barshi amma ina dan sandan yaki barinsa ya wuce sai mutumin ya bawa dan sandan naira sittin sai dan sandan yace to dauki katifanka bayan dan sandan yaje
gida yaga dakinsa bude sai yaga ashe
KATIFAR SA ce wannnan mutum ya
sato:::IDAN KAI NE, YAYA ZAKAYI???

Saturday, 8 April 2017

WAYE_MASOYINKA_NA_GASKIYA???

# LAWYER Yana fatan ka shiga matsala!!
# LIKITA Yana fatan rashin Lafiya ta sameka!!!
# POLICE Yana burin ka zama mai laifi!!!
# MAI_DORI Yana fatan ka karye!!!
# MAI_SAIDA_LIKKAFANI Yana fatan ka mutu!!!
*BARAWO* ne kawai yake fatan ya ganka cikin arziki,lafiya da wadata
(Don ya sace maka dukiyarka)
YAU NE RANAR BARAYI TA DUNIYA
Ka aikawa wani # BARAWO da ka sani
Ni ma wani ne ya yi kuskuren aiko min

KARKA GASKATASHI

Wata rana shehu yaje kasuwa, sai ya hadu da
wani
mutum shi kuma ya siyo tangaram cike da buhu,
sai yacema shehu, ka daukar man kayannan
nawa
ka kaiman gida, ni kuma zan sanar dakai wasu
abubuwa guda ukku da zasu amfaneka har
karshen
rayuwarka, shehu yace ya yarda,suna cikin tafiya
har sunyi kashi daya cikin ukku na tafiyarsu, sai
shehu yace ka fada min yanzu, sai mutumin yace,
na daya duk wanda yace maka da qoshi gara
yunwa karka gaskatashi, shehu yace to na biyu
fa?
Saiyace duk wanda yace maka da tafiya kan abin
hawa gara tafiya a qasa karka gaskatashi, bayan
sun isa kofar gidan mutumin sai shehu yace ka
fada min gudan, saiyace duk wanda yace zan
biyaka ladan daukar kayan nan karka gaskatashi,
sai shehu ya daga buhun tangaram ya rabkashi
da
kasa, sai yace duk wanda yace akwai sauran
tangaram mai rai a cikin buhunnan karka
gaskatashi

BAN BANCIN AUREN BUDURWA DA BAZAWARA

1 -BUDURUWA kayan lefe
BAZAWARAWA taburma da chingam ya isa
2 -BUDURUWA saka rana mai tsawo ta biki
BAZAWARAWA sati daya ya isa
3 -BUDURUWA buga invitation
BAZAWARA a masallaci za,a sanar ya isa
4 -BUDURUWA ba working experience
BAZAWARA akwai working
experience ta sankomai
5 -BUDURUWA sadaki 50000, 100000
BAZAWARA dubu uku ta isa 3000,zaka iya yi mata
alqawari ma kace sai bayan an daura
6 -BUDURUWA sai an jira kayan dakiπŸ›‹πŸ›πŸ–Ό
BAZAWARA already tana da su idan babu ma za ta zo haka
Gayu mu qyale YAN MATAN NAN mu koma wa
ZAWARAWA ...... ni yanzu haka dazan samu
wata bazawara ai
Daba hakaba...

LABARIN GOGA DA MALAMINSA

A makarantar su goga Malam
ya shigo aji...... Yana koyar da hausa language....
Darasi ya fara ....malam ya kammala
bayanai akan JIMLA...
sai malam yace to zai yi gwaji...wato yaga idan
daliban
sa suna fahimta...
Sai yace waye zai iya idan na kawo masa jimla sai
ya kawo
min kishiyar ta...??
Sai GOga yadaga hannu....sai malam ya fara
tambaya
kamar haka...
Malam yace: SAMA
Goga yace: kasa
Malam yace: Ruwa
Goga yace: iska
Malam yace: wuta
Goga yace: Aljanna
Malam yace: malami
Goga yace: dalibi
Malam yace: mai kudi
Goga yace: talaka
Sai malam yai murmushi yace...amma kanada
kokari
Sai Goga yace: ..amma kai dakiki ne
Sai malam yace ... To ya isa haka
Goga yace: bai isa ba
Malam yace: kanada hankali kuwa
Goga yace: mahaukaci ne kai
Malam yace: dan ubanka kai shuru
Goga yace :dan uwarka kai magana
Malam yakara cewa: nace kai shuru
Goga yace: nace kai magana
Malam yace: lallai yau zanci ubanka
Goga yace : lallai gobe zanci uwarka
** Keep share Just to make someOne Funny!!!...
Kokunga laifin Goga Anan

Labarin Sarki Da Sarauniya A Garin Mayu

Wani Sarki ne da Sarauniyarsa suke mulki a wani gari mai yawan,mayu.Duk da cewa Sarkin nan da Sarauniyarsa babu abin da suka rasa na dukiya da jin dadin zaman duniya, amma Allah bai nufe su da
haihuwa ba tsawon shekaru, har tsufa ya fara sallamo ma su.
Ana nan wata rana, sarauniyar,nan ta fita bayan gari shan iska, ita kadai, har ta iso bakin wani rafi, sai kuwa ta ga wani dan
karamin kifi ruwa ya turo shi bakin gaba, ya yi, ya yi, ya koma ciki ya kasa har yana shirin mutuwa. Sarauniya ta ji tausayinsa ta dauke shi ta mayar
da shi cikin ruwa.
Bayan kifi ya yi nitso cikin ruwa, ranshi ya dawo, sai ya dago kansa saman ruwa ya ce da Sarauniya,
"Na san abin da ke damun ku, ke da mijinki, sakamakon taimakona
da kika yi, za ki haifi 'ya mace wadda babu kamarta a kyau duk
fadin duniyar nan, sai dai wani abin al'ajabi zai faru gare ta."
Yana gama fadin haka sai ya shige cikin ruwa abinsa.
Shekara ba ta kewayo ba sai da Sarki da Sarauniya suka haifi 'ya mace, wadda ba a taba ganin
kyakkyawa kamarta ba.
Da ranar suna ta kewayo, Sarki ya gayyato
manyan Sarakuna na duniya domin taya shi murna.
Ita kuma Sarauniya ta gayyato manyan mayun kasar su goma sha biyu.
Duk baki kowa ya hallara,
Sarakuna suka cika fada, mayu kuwa kowace ta zo tana sanye da jar hula da jajayen takalmi rike da
fararen sandunansu na tsafi.
Bayan an ci biki har an kusa watsewa, bakin Sarki suka bayar da kyaututtukan da suka kawo wa abokinsu.
Su kuwa mayu sai suka fara ba wa jaririya kyaututtukan sihiri. Ta
farko ta nuna ta da sandarta ta ce,
"Za ki zama kyakkyawa." Ta biyu
ta ce, "Za ki zama mai arziki." Ta
uku ta ce, "Za ki zama mai ilimi."
Ta hudu ta ce, "Za ki zama mai
tausayi da taimako."
Haka dai suka ci gaba da ba ta kyautuka har zuwa mayya ta goma sha daya. Har mayya ta sha
biyu za ta mike ta bayar da tata kyautar, sai aka ji wuri ya hargitse da kururuwa da hayaniya da iska.
Lokacin da wuri ya natsa, kamar daga sama sai aka ga wata mayyar ta bayyana a cikin taron,
tana sanye da bakar hula da bakaken takalmi da bakar sanda.Ashe an manta ba a gayyato ta ba wurin biki, ita kuwa ta ji haushin
wannan banbanci da aka nuna mata. Sai ta nuna jaririya da bakar sandarta ta ce, "Idan ki kai shekara goma sha biyar za ki soke
hannunki da kwarashin saka, nan take za ki mutu!" Tana fadar haka
sai ta yi wata irin dariyar keta, ta zama iska ta bace.
Hankali Sarki da Sarauniya ya tashi a kan wannan fata na mayya. Ga shi abin da suke nema shekara da shekaru sun samu amma burinsu
na barin zuri'a a duniya ba zai cika ba, 'yarsu za ta mutu tun kafin ta yi aure!
Nan da nan sai mayya ta goma sha biyu, wadda ba ta bayar da kyautarta ba, ta taso ta ce da Sarki
da Sarauniya, "Hakika wannan mayya da ta fita yanzu babbar matsafiya ce, babu mai iya tare
sihirinta a nan cikinmu. Amma ni, zan yi iyakar kokarina in rage masa karfi." Sai ta nuna jaririya da sandarta ta ce, "Idan ki ka cika shekara goma sha biyar, tabbas za ki soke hannunki da kwarashi,
amma ba za ki mutu ba, za ki kwanta barci wanda ba za ki farka ba sai bayan shekara dari."
Bayan an gama biki an watse, Sarki ya sa aka sanar da dukan mutanen gari duk wanda ya san
yana da kwarashi, kai koda allura ce, a fito da su. Aka tara kwarashi
da alluran garin gaba daya aka kona su. Sarki ya sa doka mai tsanani akan shigo da kwarashi ko allura a cikin garinsa.
Da 'yar Sarki ta fara tasawa, dukan kyautukan da mayun nan suka ba
ta, suka fara bayyana tare da ita.
Ga ta dai ta zama kyakkyawar da babu kamarta, ga hikima da
basira, ga tausayi, dukan abin da aka koya mata sau daya, shi ke nan ta rike shi.
A kwana a tashi har ta kai shekara goma sha biyar cif, a daidai lokacin ne kuma tafiya ta kama
Sarki da Sarauniya zuwa wani gari. Aka bar 'Yar Sarki a gida, ita da masu kulawa da ita. Da ta gaji
da zama sai ta tashi tana bi lungu-lungu na gidan domin ta mike kafafunta.
Ta zo wani lungu, sai ta
ga wani daki da marikin kofarsa ta zinariya. Ta kama marikin kofar
ta tura, sai kofar ta bude. Ta kutsa kai cikin dakin, sai ta ga wata 'yar tsohuwa, tukuf da ita, zaune a kan kujera tana saka.
Ta kura wa 'yar tsohuwa ido, ta ga yadda take ta surkulle da kwarashi, sai abin ya burgeta. Ta matsa kusa da 'yar tsohuwa ta gaisheta cikin ladabi, ta ce da ita tana so ta koyi yadda ake wannan
abu. Ashe ba ta sani ba, 'yar tsohuwar nan ita ce mayyar da ta yi mata fatar mutuwa bayan shekara goma sha biyar.
***

Friday, 7 April 2017

Yaro Da Addu'ar Allah ya karo Mata Uku

Wani yaro ne shi da Babansa, kullum sai yace Baba ka saya min mota, Baban sai ya ce to zan kawo maka. Kullun haka sai wata rana,
Baban ya kawo mai motar. Yaron ya ce Baba na gode
Allah karama kudi da kuma
Mata guda 3. Mamarsa tana sallah ta ce ba amin ba dan ubanka πŸ˜€πŸ˜€πŸ˜€hhhhhh😬😬😁😜😜😝😬

Thursday, 6 April 2017

Kaza Da Akuya

Watarana angama ruwan sama kaza da kawarta akuya suna tafiya agefen titi sai wani mai mota🚘 yawuce aguje harya fallatsa musu ruwan kwata sai kazaπŸ“ tace Ji yadda suke gudu kamar wasu awaki🐐🐐 sai akuya🐐 tadanyi murmushi tace shiyasa suke mutuwa kamar kajiπŸ“πŸ“πŸ“
πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚

Wednesday, 5 April 2017

Mai Tallan Biredi

Wani mai tallan bread ne irin nakan titinnan mu,sai yaga bus din J5 tashiga gidan mai da daddare sai yabita da gudu kamar yanda suka sabayi,kawai sai ya miqa bread ta window sai yaji ankarba,sai yaqara mikawa sai yaji ankarbe dazai sake miqawa saiyace abani kudin biyun sai yaji shiru, kawai saiya leqa sai yaga ashe akuyoyine a bayan motar
😳😳😳😳😳😳😳
πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚
Dariya small small,
Ka tura don nishadin sauran friends

Bature Da Bagobiri

BANDA DARIYA😊
Wani Bature ne yazo Nigeria, sai Tafiya ta kamashi zuwa Sokoto, acikin tawagar da sukazo tarbonsa harda wani SSS BAGOBIRI.
Bayan sun gaggaisa sai Bature ya rike hannun Bagobiri yana Kallon fuskarsa yana mamakin irin Tsagen dake fuskar wannan Bagobirin sai yake tambayarsa. My Friend Did u Fight wit a tiger..? Sai Bagobiri cikin fushi yace No I Fight with Ubanka ne. Sai Bature ya sake Kallon Fuskar Bagobiri yace that Ubanka is a very Dangerious Animal.
Dont laugh alone, share the joke with ur friends.πŸ˜„

Labarin part 1,2,3, Da 4.

*MU KYAKYATA***
Wani saurayine yaje
xance, sai
budurwarsa ta nemi
ya bata labari, sai
yace to. amma labarin part 1, 2, 3,
da 4, sai tace ya
bata, saurayin ya
fara kamar haka
part 1: Wani mijine
da matarsa, suna cikin tafiya a mota,
can sai sukaxo
mararrabar hanya,
sai yacewa matar
wace hanya xamu
bi ? matar tace a'a dai maigida mubi
hanyar da ta bi
dama, aikuwa sai ya
kwashe ta da mari
yace nina ke tuka
motar ko kuwa ke? hanyar hagu xa
mubi, sai budurwar
ta saka dariya tace
amma wannan miji
akwai mugu,
saurayi yace saura part 2: suka bi
hanya suna tafiya
suka iso gun masu
saida kifi, maigida
ya siya musu,
matar tace maigida mai xa'ai dashi, yace
dapawa xakiyi,
aikuwa matar ta
xabgeshi da mari,
tace kaike girkin ko
ni?? Soyawa xanyi, Budurwar ta
kyalkyale da dariya,
tace amma ta
burgeni kaga sunyi
duro, saurayi yace
saura part 4, sai budurwar tace a'a
part 3 dai, saurayi
ya kwasheta da
mari, yace ni nake
bada labarin ko
ke...!! Toh wai idan kaine/
kece budurwar,
mexaki yiwa wannan
saurayin??

Dan Fulani Da Ihun Jesus

Danfulani ne ya shiga mota LUxurious daga Aba zuwa Yola,,,,,suna cikin tafiya
motar ta kwace,,,mutanen ciki sai kiran JESUS sukeyi, danfulani ma yanata kiran JESUS! Da motar ta dawo daidai sai wata mata Igbo tace "meyasa baka kira Allanka bab kake kiran JESUS?". Sai danfulani yace "shegiya shashasha aini na zata JESUS sunan direban motar NE....

Saurayi Mai Son Mata

Wani Saurayine mai son mata amma kash sai dai
yanada tsoro' domin bai san yadda zai yi magana
da budurwa ba' wata rana ya debo wankan sa na
yamma yaxo kan titi yayi tsaye kawai sai ga wata
dalleliyar budurwa ta ci kwalliya sai yace yau kam
duk abunda zai faru sai dai ys faru" kawai sai
yayi mata sallama sai tace malam lafiya???? sai
yace don Allah nawa ake sayarda buhun
shinkafa???? sai ta fahimci cewa lallai ya rudene.
amma da yake so!!!!!! baya boyuwa sai tace bani
number ka idon naje gida zan tambaya sai in
gayamaka.bayan taje gida sai ta kirashi tace
mishi I LOVE U kawai sai ta kashe waya. shine
wannan saurayi yayi tsalle ya kira kansa da suna
"""" sharukhan"

..ASIRI YATONU..

Wasu ma'aurata ne su na da yarsu guda daya yar shekara biyar wata rana suna cin abinci sai yarsu tafara basu labari....

YARINYA : MOM yau da muna dawowa daga makaranta munga DAD dawata mata,,,,

DAD : dan Allah kiyimana shiru kina cin abinci kina surutu,

MOM : kabarta tagama mana my dear cigaba
sai meyafaru?

YARINYA : sai suka shiga wani lungu
muma muka bisu muna lekasu sai yayi kiss nata
yacire mata kaya itama tacire masa kayansa
sai,,,

MOM : sai mai my dear kicigaba mana,

YARINYA : sai suka farayin abunda kukeyi da uncle ABDULL in DAD yatafi office,

MOM: rufe mana
baki ba babanki yace kidaina magana inkina cin abinciba bakyaji inkika kara magana zan buge miki baki..... 😳😳😳
LABARIN MAI DADI...
Wataran ne wani mutum
yaje wurin wa'azi sai yaji
malam na cewa:
duk wanda
ya kwanta da matansa ta
sunna toh tamkar ya kashe
arna 70 ne..
da aka tashi daga wa'azi sai ya tafi gida tin
daga kofan gida ya fara kiran
matansa, kande! kande!!
xo
ashe wanga abun lada
garesa.. sai matansa tace
maigida a'ina kaji haka? sai yace malam ne
yace kamar
mun kashe arna 70...
Da dare
yayi mutumin ya tashi
ya kashe arna 70.... ya kwanta..
can anjuma sai matarsa ta
tasheshl tace maigida tashi, sai yace me?
sai
matan tace
tashi ka kashe arna. ya tashi
ya kashe arna 70
ya kwanta...
can anjuma ma tasake tashinsa
tace mai gida tashi, sai yace
arna koh? tace eh! yatashi ya kashe arna ya
kwanta.. can
anjuma tasake cewa mai
gida tashi ka kashe arna,
yatashi da ker da ker ya
kashe arna 70 ya kwanta..
..can misalin karfe 4 na a subahi tasake
cewa
mai gida Tashi
ka kashe arna" sai yace
kande! tace na'am mai gida.
daga annabi sai wa? tace
abubakar" sai yace shima ya
mutu yabar arna..

Barayi Da Gudun Mutuwa

Wata ranane wani yaji ancemai barayi zasuzo gidanshi sata sai yarude yarasa yanda zaiyi. Sai yasai linkafani ya dinka yasa ajikinsa sai ya hau can saman gidanshi. Barayin suna shigowa sai yace "kullu nafsin za'ikatul maut, dukkan mai rai mamacine". Sai suka daga kansu sama sukagan shi. Sai yace " Azara'ilu taremun can kadasu gudu. Garin gudu rigar daya tamakale a kofa yakasa gudu yadinga ihu yana Mala'ika Jibrilu bandani, basata nazoyiba πŸ˜„πŸ˜„πŸ˜‚πŸ˜„

Tuesday, 4 April 2017